Isa ga babban shafi
Turkiya- Rasha-Ukraine

Erdogan ya bukaci sasanta rikicin Rasha da Ukraine ta hanyar lumana

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci sasanta rikicin Ukraine da Rasha cikin lumana ta hanyar mutunta Ukrain a matsayinta na kasa.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky, yayin ganawa da fadar gwamnatin Kremlin ranar 10 ga watan Afrelun 2021.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky, yayin ganawa da fadar gwamnatin Kremlin ranar 10 ga watan Afrelun 2021. via REUTERS - MURAT CETINMUHURDAR/PPO
Talla

Erdogan wanda ke tattaunawa da manema labarai bayan ganawa da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky, a Istanbul yace Turkiya na da niyyar "tabbatar da tekun Bahar Maliya ya kasance na zaman lafiya da hadin kai" a dai-dai lokacin da jiragen ruwan yakin Amurka ke shirin ratsawa ta mashigin ruwan Turkiyya.

"Ba mu son a kara samun tashin hankali a yankin da muke tare," in ji Erdogan.

 

Shugaban na Turkiyya ya kara da cewa "Mun yi imanin cewa dole ne a sasanta rikicin da ake yi ta hanyar lumana bisa tsarin kasa da kasa da mutunta yankin Ukrain."

Hukumomin Ukraine da na Amurka sun nuna damuwa ‘yan kwanakin nan,  sakamakon yadda dubban sojojin Rasha da kayan aiki suka isa wani yanki kusa da gabashin Ukraine, inda tashin hankali tsakanin‘ yan aware masu goyon bayan Rasha da kuma sojojin gwamnatin Kiev ke karuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.