Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta hukunta tsoffin sojoji saboda haddasa rikici

Gwamnatin Faransa ta jaddada aniyarta ta hukunta wasu tsoffin sojoji da suka rattaba hannu kan wata wasika mai kunshe da gargadi ga shugaban kasar Emmanuel Macron game da yiwuwar barkewar yakin basasa a kasar. Faransan ta ce ya zama dole a hukunta su, don kuwa wasikar tasu ba ta kunshi komai ba illa nuna wariyar launin fata da kuma tsattsauran ra’ayi.

Wasu sojojin Faransa
Wasu sojojin Faransa AFP - THOMAS SAMSON
Talla

A cewar fadar shugaba Macron, wasikar kanta ka iya tada rikici a kasar saboda sun nuna karara suna bukatar gwamnati ta far wa wani sashe na jama’a don kawai wariyar jinsi ko kuma tsattsauran ra’ayi irin nasu.

Wasikar ta bukaci shugaba Macron da ya dauki mataki kan jama’ar wata unguwa da suke zargin masu laifi ne.

A cikin wasikar, masu damarar sun ce matukar ba a dauki matakin kan mutanen unguwar ba, yakin basasa ka iya barkewa a kasar.

Sai dai wasikar da aka wallafa a wata mujallar kasar a ranar Talata, ta janyo hankalin mutane har ta kai ga gwamnati ta jadadda cewa, ya zama wajibi a dauki mataki a kansu saboda wasikar ba ta kunshi komai ba sai wariyar launin fata da kuma kalaman tunzuri ga jama’ar yankin da suke son a farwa.

Baya ga shugaban kasa, jam’iyya mai mulki a kasar da jam’iyyar adawa ma, sun yi Allah-wadai da abubuwan da wasikar ta kunsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.