Isa ga babban shafi
Afrika-Faransa

Macron na shirin karbar bakoncin taron tattalin arzikin nahiyar Afrika

A ranar talata mai zuwa shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai karbi bakuncin shugabannin Afirka 15, da wasu manyan jami’an kasashen Turai da na kungiyoyin kasa da kasa, domin tattaunawa kan yadda za a farfado da tattalin arzikin nahiyar Afirka.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin jawabinsa gaban manema labarai a taron EU da ya gudana a Portugal.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin jawabinsa gaban manema labarai a taron EU da ya gudana a Portugal. REUTERS - POOL
Talla

Fadar shugaba Macron ta ce manufar taron ita ce, samar da manufofi da za su taimaka wajen farfado da tattalin arzikin nahiyar, musamman lura da yadda irin ta’adin da annobar Korona ta yi masa ciki har da asarar rayukan mutane dubu 130.

Bullar wannan annobar dai ta haddasa tarnaki ga tattalin arzikin Afirka mafi muni a cikin shekaru 25 da suka gabata, to sai dai an yi hasashen zai mirmije a cikin shekara ta 2022.

Wasu daga cikin abubuwan da taron zai tattauna sun hada da yadda za a kara janyo hankulan masu saka jari zuwa Afirka, sai kuma bayar da damar is aga basusuka wadanda kudin ruwansu ba ya da nauyi sosai.

A cikin watan yuni mai zuwa ne Asusun Lamuni na Duniya IMF, zai sanar da ware kudade dala bilyan 650 a matsayin bashi ga kasashen duniya, daga cikinsu dala bilyan 34 domin nahiyar Afirka.

Wadanda za su halarci taron dai su ne shugabannin kasashen Angola, Burkina Faso, Jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, Cote d’Ivoire, Masar, Habasha da kuma Ghana. Sauran su ne Ghana, mali, Mauritaniya, Mozambique, Nigeria, Rwanda, Senegal, Sudan, Togo da kuma Tunisia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.