Isa ga babban shafi
Turai-AstraZeneca

EU ta maka AstraZeneca a kotu saboda rigakafin corona

Kungiyar Kasashen Turai ta bukaci wata kotun Belgium da ta ci tarar miliyoyin kudaden Euro ga kamfanin AstraZeneca saboda gazawarsa wajen samar da rigakafin cutar Covid-19 ga nahiyar.

EU na takun-saka da AstraZeneca
EU na takun-saka da AstraZeneca REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen na EU suka fara daukar matakin shari’a kan kamfanin har-harda magungunan na AstraZeneca saboda zargin sa da karya ka’idojin kwantiragin da ya kulla da kungiyar ta EU.

Sai dai lauyan kamfanin na AstraZeneca, Hakim Boulabah ya yi watsi da ikirarin EU, yana mai cewa, babu wata ka’idar da aka karya a kwantiragin.

EU ta dauki matakin maka kamfanin a kotu ne domin tilasta masa samar da karin rigakafin coronavirus har guda miliyan 90 kafin watan Yuli.

Hukumar Tarayyar Turai ta ce, wa’adin kwantiragin da ke tsakanin bangarorin biyu zai kare ne a tsakiyar watan Yuni, amma ta bukaci cin  tarar kamfanin muddin ya gaza cika alkawarinsa a kan lokaci.

Tawagar lauyoyin EU na son a fara bai wa nahiyar kafin-alkalami na Euro miliyan 10 a wani bangare na kudin tarar saboda  jinkirin da AstraZeneca ya yi na samar da rigakafin na Covid-19.

AstraZeneca dai ya samar da rigakafi miliyan 30 ne ga nahiyar Turai daga cikin miliyan 120 da EU ta yi alkawari da shi a tashin farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.