Isa ga babban shafi
Amurka - Florida

'Yan bindiga sun jikkata mutane 20 a Amurka

Wasu ‘yan bindiga 3 sun kashe mutane 2 tare da jikkata wasu akalla 20, bayan da suka bude wuta kan jama’ar dake halartar taron raye-raye da kade-kade a garin Miami dake jihar Florida a Amurka.

Yankin birnin Miami da 'yan bindiga suka kashe mutane 2 bayan jikkata wasu 20 a jihar Florida dake Amurka.
Yankin birnin Miami da 'yan bindiga suka kashe mutane 2 bayan jikkata wasu 20 a jihar Florida dake Amurka. CHANDAN KHANNA AFP
Talla

Wadanda suka shaida aukuwar lamarin sun ce, ‘yan bindigar sun zo wajen taron kade-kaden ne cikin wata mota kirar Nissan ida nan take suka budewa jama’a wuta, bayan ta’addancin ne kuma suka tsere cikin motar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da irin haka ke faruwa ba, sakamakon kaurin sunar da Amurka tayi wajen fuskantar hareharen na ‘yan bindiga dadi dake afkawa jama’a a wuraren da suka hada na shakatawa, makarantu, ma’aikatu da kuma kasuwanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.