Isa ga babban shafi
Faransa-Zabe

Macron ya fara ziyara a sassan Faransa gabanin babban zaben kasar

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fara rangadi a sassan kasar daga yau laraba, a wani yunkuri na tunkarar babban zaben kasar na badi, makamancin rangadin da ka iya maimaita abin da faru lokacin fusatattun masu zabe suka farwa shugaban.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. Bertrand Guay AFP
Talla

Shugaba Macron mai shekaru 43, da ke neman wa’adi na biyu a zaben Faransar da zai gudana cikin watannin Aprilu da Mayu na shekarar 2022 ya ce rangadin zai fayyace masa abin da ya ke tunkara a zaben na badi.

Tsohon ma’aikacin bankin mai tsaka-tsakan ra’ayi kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a ta baya-bayan nan ta nuna shi a matsayin kan gaba tsakanin takwarorinsu da ke kokarin fafatawa a zaben.

Macron wanda ke shirin yin tattaki har kauyukan sassan kasar na shirin daura damara don ganin rawar da jam’iyyarsa za ta taka a zaben yankuna tsakanin ranakun 20 zuwa 27 na watan nan, yayinda ya shirya gomman tafiye tafiye da nufin kara jan hankalin magoya baya.  

Tun bayan hawansa mulki Macron wanda har yanzu Marine Le Pen ta jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi ke matsayin babbar kalubale gareshi, ya gudanar da makamantan tafiye-tafiyen don neman cikakken goyon baya.

Farin jinin Emmanuel Macron ya dawo ne bayan janye dokar takaita walwalar jama’a da kuma matakan da ya dauka a yaki da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.