Isa ga babban shafi
Jamus-Ambaliyar ruwa

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 81 a Jamus

Akalla mutane 81 suka rasa rayukansu a Jamus sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu kasashen yankin Turai, yayin da gidaje da dama suka ruguje.

Ambaliyar ruwam ta rusa gidaje da dama
Ambaliyar ruwam ta rusa gidaje da dama AP - Roberto Pfeil
Talla

A wani yanayi da ba a saba ganin irinsa ba, ambaliyar ruwan ta mamaye kasashen Luxembourg da Netherlands da kuma Belgium masu makwabtaka da Jamus.

Jihohin Rhineland-Palatinate da North Rhine-Westphalia da ke Jamus sun fi dandana ibtila’in ambaliyar ruwan wadda ta haddasa tunbatsar koguna, abin da ke kara barazana ga rugujewar gidaje.

An tura kimanin sojoji 400 domin kai dauki a wadannan jihohi guda biyu, inda kuma aka rawaito akalla gidaje dubu 135 sun rasa wutar lantarki a jihohin kadai.

A can birnin Leverkusen kuwa, katsewar lantarkin ta tilasta kwashe majinyata 468 daga asibitin da suke samun kulawa.

Baya ga gomman mutanen da jami’an tsaro suka tabbatar da mutuwarsu, har yanzu akwai daruruwan mutane da suka bace a sanadiyar ibtila’in.

Mutane da dama sun yi ta darewa kan rumfunan gidajensu domin tsira da rayukansu, inda kuma jirage masu saukar ungulu suka rika kwashe su don isar da su tudun-mun-tsira.

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce, ta kadu matuka da aukuwar ambaliyar ruwan, tana mai mika godiya ga masu aikin ceto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.