Isa ga babban shafi

Shekaru 40 na fara amfani da jiragen kasa a Faransa

Faransa ta gudanar da bikin cika shekaru 40 na fara amfani da jiragen kasa masu sauri dake zirga zirga zuwa yankunan karkarar kasar, yayin da ake shirin kaddamar da wasu sabbin jiragen da zasu fara aiki daga shekarar 2024.

Shugaban Faransa emmanuel Macron a tashar Gare de Lyon na Paris
Shugaban Faransa emmanuel Macron a tashar Gare de Lyon na Paris AP - Michel Euler
Talla

Hukumar dake kula da layin dogo ta Faransa da aka sani da SNCF  a yau juma’a ta yi bikin  cika shekaru 40 da kafuwa, bikin da Shugaban kasar Emmanuel Macron ya halarta tareda rakiyar wasu daga cikin mukaraban sa a tashar jiragen kasa dake birnin Lyon.

A shekara ta 1981 ne tsohon Shugaban kasar marigayi Georges Pompidou ya kaddamar da ayyukan gina layin dogo a Faransa, ayyukan da Valery Giscard D’Estaing da ya shugabanci kasar ta Faransa bayan Pompidou ya  karasa.

Tashar jiragen kasa na Lyon dake Faransa
Tashar jiragen kasa na Lyon dake Faransa AP - Michel Euler

 

Shugaba Francois Mitterand ne ya jagoranci bikin  bude hukumar  ta SNCF a lokacin.

Wanda kama daga lokacin zuwa wannan rana da ake bikin cika shekaru 40 da kaddamar da hukumar layin dogon Faransa ta SNCF  mutane bilyan uku ne suka shiga jiragen kasa da sunan fasinja a kasar.

Shugaba Emmanuel Macron yayi amfani da bikin da aka yi a Gare de Lyon dake birnin Paris inda shugaba Francois Mitterand ya kaddamar da jiragen TVG a shekarar 1981 wajen gabatar da shirin da yake da shin a inganta sufurin jiragen kasa a Faransa.

 

Jirgin kasa na hukumar SNCF a Faransa
Jirgin kasa na hukumar SNCF a Faransa AFP - BERTRAND GUAY

 

A gaban mahalarta taron shugaban ya jinjinawa shirin kasar da kuma bayyana yadda zai zuba jarin euro biliyan 6 da rabi wajen inganta sufurin jiragen kasa, ciki harda samar da sabbin layin dogo tsakanin biranen Nice da Toulouse.

Zamu ci gaba da inganta wannan bangare ta hanyar zuba jarin makudan kudade domin bunkasa bangaren masana’antun mu tunda mutane na bukatar sabbin hanyoyin sufuri masu inganci a kanana da manyan birane.

 

Shugaba Emmanuel Macron a tashar gare de Lyon
Shugaba Emmanuel Macron a tashar gare de Lyon AP - Michel Euler

 

Ana saran sabbin jiragen masu sauri su dauki fasinjoji da yawa da zasu kai 740 maimakon 600 da ake diba yanzu, da kuma amfani da hasken wutar lantarki kasa da kashi 20 da ake amfani da shi yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.