Isa ga babban shafi
Faransa

Al'ummar Faransa sun rarrabu kan hukuncin kisa shekaru 40 bayan soke shi

Faransa ta yi bikin cika shekaru 40 da soke hukuncin kisa, matakin da tsohon shugaban kasar François Mitterrand ya goyi baya a waccan lokaci.

Zauren Majalisar Dokokin Faransa.
Zauren Majalisar Dokokin Faransa. © REUTERS/Benoit Tessier/File Photo
Talla

Sai dai bayan kwashe gwamman shekarun da soke zartas da hukuncin na kisa, wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewar, a halin yanzu kusan kashi 50 na al’ummar Faransa na neman sake maido da hukuncin.

Bayanai dai sun nuna cewar lokacin da Majalisar Dokokin Faransa ta kada kuri'ar soke hukuncin kisa shekaru 40 da suka gabata, sama da kashi 60 cikin 100 na al'ummar kasar ke adawa da matakin.

A ranar 18 ga Satumban shekarar 1981, ‘yan majalisar Faransa 363 suka kada kuri’ar soke dokar hukuncin kisa a kasar, yayin da 117 suka hau kujerar na ki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.