Isa ga babban shafi
Amurka - Faransa

Biden da Macron sun tattauna kan karfafa tsaron nahiyar Turai

Shugaban Amurka Joe Biden da takawaransa na Faransa Emmanuel Macron sun tattauna batun karfafa tsaron nahiyar Turai yau Juma’a, a dai dai lokacin da Amurkar ke kokarin inganta dangantaka da kasar bayan rikicin da ya biyo bayan kwangilar jiragen yakin karkashin teku.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Amurka Joe Biden.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Amurka Joe Biden. AFP - PHIL NOBLE
Talla

Sanarwar da fadar shugaban Amurka ta gabatar tace shugaba Biden da Macron sun tattauna muhimmancin samar da tsaro mai inganci a nahiyar Turai tare da rawar da kungiyar NATO ke takawa.

Wannan tattaunawa da shugabannin suka yi ta waya na zuwa ne a dai dai lokacin da Amurka ke kokarin inganta danganta da kasar bayan barakar da aka samu wajen karbe kwangilar ginawa Australia jiragen yakin karkashin teku da kasar tayi, bayan kulla yarjejeniya da Faransa.

Sanarwar tace shugaba Biden zai gana da Macron a birnin Rome a cikin wannan wata, inda shugabannin zasu tattaunawa batutuwan ci gabada dama.

Fadar Amurkar ta kuma ce mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris zata ziyarci Faransa a watan gobe domin bunkasa hadin kan kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.