Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

Isra'ila za ta gina matsugunan Yahudawa sama da 1,300 a yankin Falasdinu

Isra’ila ta bayyana shirinta na gina karin gidaje sama da dubu daya da dari 3 don tsugunar da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna a yankin yamma da tekun Jordanda ta mamaye.

Fiye da Yahudawa dubu 600,000 ke zaune a yankin yamma da kogin Jordan ba bisa ka'ida ba.
Fiye da Yahudawa dubu 600,000 ke zaune a yankin yamma da kogin Jordan ba bisa ka'ida ba. MENAHEM KAHANA afp/AFP/File
Talla

Sanarwar da ta fito daga ma’aikatar samar da  gidaje  ta gwamnatin Fira minista Naftali Bennett ta ce an bada ayyukan gina gidaje guda dubu 1 da dari 3 da 55 a yamma da kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye tun a shekarar 1967 da aka yi yakin kwanaki 6.

Wadannan sabbin gidaje, kari ne a kan sama da gidaje 2000, wadanda majiyoyin tsaro suka ce za a ba mazauna cikinsu  takardun izinin zama a yankin, lamarin da  ya janyo caccaka daga Falasdinawa, masu fafutukar lalubo zaman lafiya da kuma makwafciyarta, Jordan.

A wata sanarwa, ministan samar da gidajen Isra’ila Zeev Elkin, wanda dan jam’iyyar New Hope party mai ra’ayin mazan jiya ne, ya ce jaddada kasancewar Yahudawa a yamma da kogin Jordan yana da mahimmancin ga manufofin akidar Zionism.

Da yake jawabi a taron mako mako na majalisar zartaswar Falasdinawa, Firaminista Mohammed Shtayyeh ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da musamman ma Amurka da su tinkari Isra’ila a kan wannan mataki da take daf da dauka.

Kimanin Yahudawa dubu 475,000 ne suka share wuri suka zauna a Yamma da kogin Jordan, inda Falasdinawa ke kallo a matsayin makomarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.