Isa ga babban shafi
Faransa

An gano kayayyakin yaki masu tarihi a wani yanki na Faransa

Hukumomi a Faransa sun sami wasu baraguzan makamai da alburusai da kuma alamun kayayyakin yakin wasu kasashe na tarihi a yankin Normandy wajen da aka karkare yakin duniya na biyu.

Yankin gabar tekun Normandy a ranar 6 ga watan Yunin 1944.
Yankin gabar tekun Normandy a ranar 6 ga watan Yunin 1944. AFP/File
Talla

Bayanai sun ce jami’an tsaron Faransan ne suka gudanar da bincike don gano kayayyakin tarihin.

Hukumomin kasar sun ce batun fara binciken ya samo asali ne bayan da hukumomi suka kama wani mutum dan shekaru 25 dauke da irin wadannan kayayyaki kuma ya ki baiwa jami’an tsaro damar bincikar sa.

An dai kama matashin ne dauke da irin wadannan tsaffin makaman a yankin na Normandy, abin da ya bai  wa hukumomi damar fara binciken neman kayayyakin a yankin.

To amma a cewar hukumar binciken ababen tarihi ta Faransa samo wadannan kayayyakin abin farinciki ne ga kasar har ma da inganta bangaren alkinta tarihin ta.

Sai dai har yanzu hukumomi basu bayyana adadin kayayyakin yakin da suka samu ba, amma dai bayanan da jaridar Daily Monde ta fitar na bayyana cewa akwai Manyan bindigogi guda 130 da suka hadar da kirar AR-15 da AK 47 sai kuma bindigogi masu sarrafa kansu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.