Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Rasha na son fadada karfinta a Turai

Shugaba Vladmir Putin na Rasha, ya jaddada cewa fadada kungiyar tsaro ta NATO zuwa gabashin Turai abu ne mai matukar muhimmanci ga Rasha, musamman wajen kare sha’anin tsaronta.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha
Shugaba Vladimir Putin na Rasha Valery SHARIFULIN SPUTNIK/AFP
Talla

Shugaba Putin, wanda ke magana a bainar jama'a a karon farko tun bayan ganawar da ya yi da shugaban Amurka Joe Biden, ya ce Rasha na da damar kare al’amuran tsaronta.

A yayin taron nasu ta kafar bidiyon intanet, Biden ya gargadi Putin game da martanin da Rasha za ta fuskanta, musamman ta fuskar tattalin arziki daga yammacin Turai, matsawar ta kai hari ga makwabciyarta wato Ukraine.

Ana dai kallon tattaunawar a matsayin wata dama ta rage tashin hankali a kan iyakar Rasha da Ukraine, inda fadar Kremlin ta jibge dakaru 100,000, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar wani babban yaki.

Koda yake a jawabin da Mista Putin ya gabatar wa manema labarai, ya ce Rasha na da manufofin ketare cikin lumana, amma tana da 'yancin kare tsaronta, sai dai ya ki cewa ko Rashan ta shirya tura dakaru masu tarin yawa a kan iyakar Ukraine da ke kan iyaka, amma ya ce kallon yadda NATO kawai take matsowa kusa da Rasha zai zama akwai bukatar shirin ko ta kwana.

A ranar Laraba nan ne Faransa ta ce ta aike da sakwanni masu karfi ga Rasha tana mai gargadin cewa ta kuka da abin da zai biyo baya idan ta kai hari kan Ukraine.

Sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta zo ne bayan tattaunawa ta wayar tarho a wannan makon tsakanin shugabannin Faransa, Jamus, Italiya, Burtaniya da Amurka.

Ta ce, a cikin tattaunawar da suka yi, na kawancen kasashen yamma biyar sun bayyana aniyarsu ta ganin an mutunta ‘yancin kasar Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.