Isa ga babban shafi
Amurka

Dan sandan da ya kashe Floyd ya amsa laifin take hakkinsa

Derek Chauvin, tsohon dan sandan birnin Minneapolis, farar fata da aka samu da laifin kashe Ba’amurke bakar fata George Floyd, ya amsa laifin take hakkin dan adam abinda ya janyo masa aikata laifin kisan kai da gangan.Karo na farko kenan da Chauvin ya amince da aikata laifi a shari’ar da ya fuskanta.

Derek Chauvin, wanda ya amsa laifin da ake tuhumarsa na kashe George Floyd.
Derek Chauvin, wanda ya amsa laifin da ake tuhumarsa na kashe George Floyd. - Court TV/AFP/File
Talla

Mutuwar Floyd, da wani dan kallo ya dauki hoton yadda ta auku a wayarsa ta hannu, ta haifar da zanga-zangar kin jinin zaluncin da ‘yan sanda suka fi yi wa Amurkawa Bakar fata, da aka yi wa take da ‘Black Lives Matter’ tsawon watanni a fadin Amurka da ma wasu kasashen.

Chauvin ya amsa aikata laifin na take hakkin dan Adam ne jiya Laraba a gaban kotun da ke St. Paul, a Minnesota, a shari’ar da ake tuhumar sa da amfani da karfin da ya wuce kima ta hanyar danna gwiwarsa a wuyan Floyd har tsawon kusan mintuna 10 da gangan a ranar 25 ga Mayu na shekarar 2020 har sai da ya mutu, tuhumar da ya ce ba shi da ja a kanta.

Chauvin ya kuma amsa laifinsa take hakkin wani yaro dan shekara 14 a wata shari'a ta daban, a kan laifin da ya aikata a shekarar 2017, inda ya sanya wa yaron ankwa tare da danna fuskar sa kasa, ya kuma dake shi a kansa sau da dama, da wata fitila da ke hannunsa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan Shari’ar Amurka Merrick Garland ya ce duk da cewa babu abinda zai iya gyara barnar da tsohon dan sanda Derek Chauvin ya aikata, ma'aikatar shari'ar Amurka ta kuduri aniyar daukar matakin hukunta dukkanin wadanda suka saba wa kundin tsarin mulkin kasar, za kuma ta tabbatar da kare hakkin Amurkawa baki daya.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Yunin da ya gabata aka samu Derek Chauvin da laifin kisan George Floyd tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 22 da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.