Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Rasha Ukraine da OSCE za su dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta a Kiev

Kasashen Rasha da Ukraine tare da kungiyar tsaro da hadin kan Turai wato OSCE sun amince da dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta a rikicin gabashin Ukraine wanda Kiev ke yakar ‘yan awaren da Moscow ke marawa baya, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da shugaba Vladimir Putin ke bayyana yiwuwar samun kyakkyawan sakamako a tayin da ya yiwa Amurka kan rikicin.

Wani Yanki na Ukraine da ke fuskantar matsalar tsaro.
Wani Yanki na Ukraine da ke fuskantar matsalar tsaro. REUTERS
Talla

Kankanin lokaci bayan da Rasha ta mamaye yankin Crimea na Ukraine a shekarar 2014 ne Kiev ta fara fama da matsalar rashin tsaro daga yankuna biyu da ke gab da Moscow kuma tun daga wancan lokaci ta ke yaki da ‘yan tawayen yankin wadanda ke samun goyon bayan Rasha.

Kasashen yamma na zargin Rasha da girke dakaru akalla dubu 100 akan iyakarta da Ukraine a wani yunkuri na mamaya a lokacin hunturu, matakin da ya sanya Amurka gargadin dadaddiyar makiyiyarta ta mai fama da tarin takunkuman kasashen Duniya kan cewa matukar ta kaddamar da farmaki kan Kiev kai tsaye za ta janyowa kanta karin takunkumai.

Sai dai shugaban ofishin na OSCE a Ukraine Mikko Kinnunen ya ce dukkanin bangarorin da ke cikin rikicin na Rasha da Ukraine sun amince da fara tattaunawa don sabunta yarjejeniyar tsagaita wutar ranar 22 ga watan Yulin 2020.

Kungiyar ta OSCE ta ce matakin shirin fara sabunta yarjejeniyar tsagaita wutar ta biyo bayan ganawar jami’anta da mahukuntan bangarorin biyu dai dai lokacin da fargaba ke ci gaba da tsananta na yiwuwar Rashan ta sake mamayar wani yanki na Ukraine.

A bangare guda shugaba Vladimir Putin na Rasha yayin wani shirin kai tsaye na tambaya da amsa da ya ke gudanarwa a duk karshen shekara, ya ce akwai fatar samun nasara a wasikar da kasar ta aikewa Amurka wadda ta gindaya sharudda don dakile barazanar NATO gareta da kuma yadda za a warware rikicin yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.