Isa ga babban shafi
Amurka - Rasha

Amurka ta zargi Rasha da kitsa makircin samun damar mamaye Ukraine

Amurka ta zargi Rasha ta tura gungun mayakan da suka kware wajen kai hare-hare da bama-bamai zuwa kan iyakar ta, domin shirya makarkashiyar da za ta rika a matsayin hujjar afkawa makwafciyarta Ukraine da yaki, kasar da a yanzu haka ke kokarin murmurewa daga hare-haren kutsen da aka yiwa gwamnati cikin shafukanta na Intanet.

Tankar yakin sojojin Rasha yayin atasaye a yankin Kadamovskiy da ke kudancin kasar.
Tankar yakin sojojin Rasha yayin atasaye a yankin Kadamovskiy da ke kudancin kasar. © AP
Talla

Zargin da Amurka ta yi wa Rashan dai, ya sake karfafa zaman tankiyar da ke tsakaninsu akan Ukraine, mako guda kacal da fara tattaunawar sulhunta tsamin dangantakar Diflomasiyyar da ta kunno kai.

Rasha wadda a yanzu haka ta girke dakarunta akalla dubu 100 a kusa da iyaka da Ukraine, ta gindayawa Amurka da sauran manyan kasashen duniya sharadin cewa ba za su bari Ukraine ta shiga cikin kungiyar tsaro ta NATO ba.

Yayin da take karin bayani akan bayanan sirrin da ta tattara, fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce tuni Rasha ta tura wasu mayaka zuwa gabashin Ukraine wadanda ta baiwa umarnin kaiwa dakarunta farmaki, abinda za ta yi amfani da shi a matsayin hujjar tuhumar Ukraine da ka iya kai wa ga afka mata da yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.