Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

An kashe mana sojoji kusan 500 a Ukraine - Rasha

A karon farko Rasha ta bayyana cewa, kusan sojojinta 500 aka kashe a yakin da take yi da Ukraine, yayin da take ci gaba da shan matsin lamba daga kasashen duniya domin ganin ta gaggauta kawo karshen hare-harenta a kasar.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin AP - Pavel Golovkin
Talla

Sanarwar na zuwa ne bayan mako guda da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi shelar kaddamar da luguden wuta akan makwabciyarsu Ukraine.

Mai Magana da yawun Ma’aikatar Tsaron Rasha, Igor Konashenkov ya ce, baya ga sojojinsu 498 da suka mutu a fagen-daga, har ila yau akwai karin sojoji dubu 1 da 597 da suka samu raunuka a wannan yakin da suke yi da Ukraine.

Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwa da Ukraine ta fitar, inda ta yi ikirarin cewa, Rasha ta yi asarar sojojin da yawunsu ya zarta dubu 5 da 700, sannan ta ce, ta kuma  kama kimanin sojojin Rasha 200 a matsayin fursunonin yaki.

A can baya dai, gwamnatin Rasha ta gasgata cewa, lallai ta yi asarar wasu sojojinta, amma ba ta bayar da alkalumansu ba, sai a wannan karo.

A bangare guda, kungiyoyi masu zaman kansu a Rasha sun ce,  gwamnatin ta Rasha ta tilasta wa wasu mutane shiga cikin wannan yakin bayan ta yi musu rajistan dole a matsayin sabbin sojojin kasar, amma Ma’aikatar Tsaron kasar ta ce, sam al’amarin ba haka yake ba.

Rasha dai ta ce, sojojinta na ci gaba da aiki tukuru domin ganin sun kakkabe akidar ‘yan Nazi daga zukatan ‘yan Ukraine.

Ukraine ta ce, sama da fararen hularta 350 ne aka kashe tu bayan fara yakin a ranar Alhamis da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.