Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Rasha na son shafe kasarmu - Ukraine

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da kokarin shafe kasarsa da kuma tarihinta, yayin da Kungiyar Tarayyar Turai ta lafta takunkumai kan wasu manyan jami’an sojin Belarus saboda yadda suke nuna goyon-baya ga Rasha wadda ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a Ukraine.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a fagen-daga
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a fagen-daga © Internet
Talla

Sojojin sun hada da manyan Janar-Janar na Belarus shida da kuma Kanar-Kanar 16, inda aka shigar da sunayensu cikin bakin-kundin Kungiyar Tarayyar Turai saboda gudun-mawar da suka bai wa Rasha a farmakin da take kai wa Ukraine.

Daga cikin takunkuman da aka lafta musu, har da hana su shiga cikin shiyar kasashen Kungiyar Tarayyar Turai, yayin da kuma aka daskarar da kadarorinsu da ke shiyar.

A bangare guda, rahotanin baya-bayan nan cewa, fada ya kaure a cikin unguwanni bayan wasu sojojin kundunbala na  Rasha sun dira cikin birnin Kharkiv, wanda shi ne na biyu mafi girma a Ukriane, inda aka ce, sun lalata gine-ginen  ‘yan sanda da na makarantun jami’a.

Wannan na zuwa ne kwana guda da Rasha ta yi rugu-rugu da wasu gine-ginen ofisoshin kananan hukumomi da ke birnin na Kharkiv.

Kazalika dakarun Rasha sun yi ikirarin mamaye birnin Kherson da ke kusa da tekun Black Sea a yankin kudancin Ukraine, amma magajin birnin ya musanta wannan ikirari, yana mai cewa, har yanzu, birnin na nan a hannun gwamnatin Ukraine.

Har ila yau, an bada rahoton cewa, an kashe mutane biyar a wani farmaki da aka kai wa hasumiyar gidan takabijin na Kyiv da ke Babi Yar, inda a nan ne ‘yan Nazi suka yi wa Yahudawa sama da dubu 33 kisan kiyashi a lokacin yakin duniya.

Tuni sama da mutane dubu 836 suka tsere daga kasar ta Ukraine saboda wannan yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.