Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

'Manufar Putin ita ce kwace gwamnatin Ukraine'

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi amanna cewa, rikicin Ukraine zai yi mummunar kazancewa nan gaba, bayan wata ganawa da ya yi ta tsawon mintina 90 da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, wanda alamu ke nuna cewa, manufarsa ita ce, mamaye Ukraine baki dayanta.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin © Sputnik/Aleksey Nikolskyi/Kremlin via REUTERS
Talla

Daya daga cikin makusantan shugaba Macron da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce,  a yayin tattaunawar, shugaba Putin ya jaddada aniyarsa ta ganin ya kakkabe akidar ‘yan Nazi daga zukatan ‘yan Ukraine kuma ya hakikance cewa, akan gaskiyarsa yake kaddamar da farmaki.

Rahotannin baya-bayan nan na cewa, sojojin na Rasha sun yi wa Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine luguden wuta, abin da masu shigar da kara na Majalisar Dinkin Duniya ke bincike a kai saboda yiwuwar aikata laifukan yaki.

Kazalika sojojin na Rasha sun yi ruwan wuta kan birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa, yayin da suka karbe iko da birnin Kherson da ke kusa da gabar tekun Black Sea a kudancin Ukraine.

A bangare guda, Faransa ta ce, ta kwace wani katafaren jirgin ruwa mallakin wani babban jami’in gwamnatin Rasha mai kusanci da shugaba Vladimir Putin wato, Igor Sechin.

Faransa ta kwace jirgin ruwan ne a gabar ruwan Riviera sakamakon takunkuman da Kungiyar Tarayyar Turai ta kakaba wa Rasha.

Tuni dai wakilan Ukraine suka fara zaman tattaunawa ta biyu da Rasha da zummar cimma matsaya kan tsagaita musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.