China ta ce ba ta goyon bayan abin da zai ta'azzara rikicin Ukraine da Rasha
Ministan harkokin wajen China Wang Yi ya shaida wa takwaransa na Amurka ta wayar tarho cewa kasarsa ba ta goyon baya duk wani abin da zai kara azazzala rikicin da ake a Ukraine.
Wallafawa ranar:
Wang ya yi kira da a zauna a teburin sasantawa, tare da samar da daidaito a tsarin tsaron Turai don warware wannan rikici.
Ya ce kamata ya yi Amurka da nahiyar Turai ta mayar da hankali a kan mummunan tasirin da fadada kungiyar tsaro ta NATO zuwa gabashin Turai zai yi a kan tsaron Rasha.
Shi ko Blinken cewa ya yi, duniya ta wage ido tana kallon kasashen da suka tashi don kare manufofin ‘yancin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu