Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Rasha da Ukraine sun cimma matsaya kan fararen hula

Rasha da Ukraine sun amince da matakin bude hanyoyin jin-kai domin bayar da damar kwashe fararen hula da ke cikin firgici sakamakon yakin da kasashen biyu ke gwabzawa.

Wasu masu neman ficewa daga Ukraine
Wasu masu neman ficewa daga Ukraine AFP - LOUISA GOULIAMAKI
Talla

A yayin da yakin da kasashen biyu ke gwabzawa ya shiga rana ta 14, yanzu haka ana kan bude wasu hanyoyin ficewa daga biranen Ukraine da suka hada da babban birnin Kyiv wanda ya sha ragargaza sosai daga sojojin Rasha da suka yi masa luguden wuta ta jiragen sama.

‘Yan Jaridar AFP sun rawaito cewa, sun hangi sojojin Rasha a wannan rana ta Laraba suna gab da shiga cikin birnin na Kyiv, yayin da gwamnatin Moscow ke zargin Amurka da kaddamar da yakin tattalin arziki a kanta ta hanyar lafta mata jerin takunkumai.

Shugaban Ukraine Volodmyr Zelensky na ci gaba da mika kokon bararsa ga kasashen yammacin duniya domin su gaggauta amincewa da bukatar kasar Poland wadda ta ce, za ta bada gudunmawar jiragen yaki ga Ukraine bayan da Amurka ta ki amincewa da wannan bukata a farko.

A bangare guda, kimanin mutane miliyan 2 da dubu 200 ne suka tsere daga gidajensu na Ukraine, inda suka tsallaka zuwa wasu kasashe sakamakon hare-haren na  Rasha, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin matsalar kwararar ‘yan gudun hijira mafi muni da aka gani tun bayan yakin duniya na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.