Isa ga babban shafi

Birtaniya ta hana yukunrin saida Chelsea

An dakatar da cinikin kungiyar Chelsea kamar dai yada mammalakin wannan kungiya dan kasar Rasha  Abramovich  ya bukaci a yi a baya.Daukar wannan mataki daga gwamnatin Birtaniya na zuwa ne bayan da hukumomin  suka dau wasu sabin takunkumai  sanadiyyar yaki da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine.

Yan wasan kungiyar Chelsea
Yan wasan kungiyar Chelsea AP - Hassan Ammar
Talla

Mammalakin Chelsea na daga cikin  mutane bakwai attajirai da aka saka jerryn sunayen su  daga cikin mutanen dake da kusanci ga Shugaban Rasha Vladmir Poutine da kuma aka sanyawa takunkumai a yau alhamis a Birtaniya.

Tun bayan da Rasha ta kaddamar da wannan mamaya  zuwa Ukraine, mammalakin wannan kungiya ta Chelsea duk da nuna damuwar sa  a kai, Abramovich dan shekaru 55 babu sunan sa daga cikin mutanen da suka fuskanci wata barrazana daga kasashen Duniya.

Dan wasan gaba na Chelsea Chiristian Pulisic rike da kambin gasar European Super Cup da kungiyar sa ta dauka bayan doke Villarreal a watan Agustan 2021
Dan wasan gaba na Chelsea Chiristian Pulisic rike da kambin gasar European Super Cup da kungiyar sa ta dauka bayan doke Villarreal a watan Agustan 2021 Action Images via Reuters - JASON CAIRNDUFF

Soke batun cinikin wannan kungiya ta Chelsea  da gwamnatin  Birtaniya ta yi na zuwa a wani lokaci da Rasha duk da zaman tattaunawa da aka soma,na saka attajirin Abramovich cikin wani yanayi marar kyau,duk da cewa gwamnatin Birtaniya ta sanar da daukar wasu jerryn matakai na yin sassauci ga kungiyar ta Chelsea tare da bata damar ci gaba da taka tamola a fagen gasar ta Frimiya ta Ingial.

A karshe yanzu kam kungiyar ta Chelsea na fatan shiga tattaunawa da hukumomin Birtaniya don ganin an cimma mafita a kan wannan matsalla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.