Isa ga babban shafi
Faransa

Ana zanga-zanga a Faransa saboda wani dan-raji

Wata mummunar zanga-zanga ta barke a garin Corsica na Faransa sakamakon zargin da jama’a ke yi kan cewa ana cin zarafin Dan gwagwarmayar kwato hakkin dan adam din nan dake tsare a gidan yari tun shekarar 2003 wato Yvan Colonna.

Jama'a dauke da hoton Yvan Colonna
Jama'a dauke da hoton Yvan Colonna AFP - PASCAL POCHARD-CASABIANCA
Talla

Al’ummar garin na wannan zanga-zanga ne don nuna fushin su game da cin zarafin dan gwagmayar kwato hakkin Dan adam Yvan Colonna da ke tsare a gidan yari tun shekarar 2003.

Tun farko dai an yanke masa hukuncin daurin rai da rai ne sakamakon kama shi da hannu a kisan magajin garin wato Corsica, Calude Erignac, bayan lakada masa  duka, abinda ya yi sandiyyar shigar sa dogon suma kafin daga bisani ya mutu a ranar 2 ga watan Maris din 1998 wannan shekara.

Yvan wanda ke tsare a wani gidan yari dake Kamaru kuma jama’ar garin na samun labarin cewa yana fuskantar muzgunawa da kuma cin zarafi a gidan yarin, abin da ya tashi zanga-zangar.

Tun farko dai a cewar kafafen yada labaran cikin gida jama’a sun fusata ne bayan samun rahoton Mutuwar Yvan saboda karancin Iska wadda aka hana shi da gan-gan a gidan yarin, sai dai kuma daga baya hukumomin gidan yarin sun musanta batun mutuwar tasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.