Yakin Rasha da Ukraine
Magajin garin birnin Kyiv ya soke dokar hanar fita
Magajin garin Kyiv babban birnin kasar Ukraine Vitali Klitschko, ya sanar da soke dokar hana fitar da yayi shelar cewa za ta fara aiki a ranar Lahadi.
Wallafawa ranar:
Talla
Magajin garin ya bayyana haka ne ta shafinsa na Telegram ba tare da yayi karin bayani ba.
Sau da dama ne dai aka kafa dokar hana fita a birnin Kyiv tun bayan da Rasha ta kaddamar da yaki kan Ukraine a karshen watan Fabarairu.
Dokar hana fita ta karshe da ta gabata a Ukraine, ta shafe awanni 35 tana aiki a tsakanin ranakun 21 da 23 ga Maris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu