Isa ga babban shafi
Rasha - Ukraine

Rasha za ta mayar da hankalinta zuwa gabashin Ukraine

Rasha ta yi ikirarin cewa ta kammala kashi na farko na abin da ta kira sintierin soji da ya kai ta Ukraine, inda ta ce za ta mayar da hankali ne a kan ceto yankin Donbas na gabashin Ukraine bdin.

Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Shugaban Rasha Vladimir Putin. AP - Alexei Nikolsky
Talla

Sanarwar ta juma na nuni da cewa Rasha za ta takaita aniyarta a Ukraine bayan da ta fuskanci turjiya daga dakarun kasar da suka hada da fararen hula a watan farko na wannan yaki, kamar yadda rahotanni a kafafen yada labaran yamma ke cewa.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ‘yan awaren da ke samun  goyon bayan gwamnatin shugaba Vladimir Putin ne ke rike da kashi 93 na yankin Luhansk, da kashi 54 na yankin Donestk.

Babban hafsan hasoshin sojin Rasha, Sergei Rudskoi na cewa sun gama aininhin kashi na farko na dalilin shigarsu Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.