Rasha ta zargi Azarbaijan da karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Karabakh
Rasha ta zargi Azabaijan da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta hanyar shiga yankin da a yanzu ke karkashin kulawar dakarunta na wanzar da zaman lafiya a yankin Nagorno-Karabakh, inda Azerbaijan din ta gwabza yaki da Armenia kan mallakarsa.
Wallafawa ranar:
Karon na farko kenan da Rasha ta fito fili ta dora laifin karya yarjejeniyar tsagaita wutar ta 2020 kan Azerbaijan.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta kuma zargi sojojin kasar ta Azarbaijan da yin amfani da jirage marasa matuka da Turkiyya ta kera wajen kai farmaki kan dakarun Armenia a Karabakh.
Sai dai ma'aikatar tsaron Azerbaijan ta musanta zargin da Rasha ke mata, inda tace Armenia ce ke yunkurin tada hankali ta hanyar kin janye sojojinta daga yankin na Karabakh.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu