Isa ga babban shafi
Rasha-Turai

Kasashen Turai sun fara tanadin gas saboda Rasha

Kasashen Faransa da Jamus na shirin lalubo matakin da za su dauka na samar wa kansu iskar gas idan Rasha ta katse wadda take ba su suna amfani da ita sakamakon takaddamar da ta taso wajen kudin da ya da ce ayi amfani da shi wajen biyan ta.

Wata cibiyar sarrafa iskar gas aTurai
Wata cibiyar sarrafa iskar gas aTurai AP - Michael Sohn
Talla

Ministan Tattalin Arzikin Faransa Bruno Le Maire ya bayyana haka bayan da shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ba zai karbi Dalar Amurka ko Euro na kasashen Turai ba wajen cinikin iskar gas daga kasashen da basa ga maciji da juna yanzu haka.

Le Maire ya ce ganin Rasha na iya katse samar da gas din a kowanne lokaci, ya dace su samar wa kansu mafita dangane da lamarin.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana cewar ba za su biya Rasha da wani kudi da ya saba wa Euro ko dala ba kamar yadda kasar take bukata.

Shugaba Vladimir Putin ya sanar da cewar ya zama wajibi duk wata kasar da bata jituwa da Rasha, cikin su harda kasashen Turai su kafa asusun ajiya na kudin kasar Ruble domin biyan iskar gas da zasu saya daga watan Afrilu mai zuwa.

Putin yace ya zama dole kasashen su bude irin wannan asusu da bankunan Rasha wanda zasu dinga amfani da shi wajen biyan makamashin daga gobe juma’a 1 ga watan Afrilu ko kuma kasar ta katse hanyar tura musu iskar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.