Isa ga babban shafi
Rasha - Ukraine

Rasha ta sha alwashin karbe ikon kudanci da gabashin Ukraine

Rasha ta sha alwashin karbe iko da gabashi da kudancin Ukraine, sai dai mahukuntan Ukraine din sun kudiri aniyar dagiya don ceto kasarsu, a yayin da majalisar dinkin duniya ta ce gwamman fararen hula ne aka kashe a yanki guda.

Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Shugaban Rasha Vladimir Putin. via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Gwamnatin Ukraine, wadda ke samun kwarin gwiwa daga taimakon sojin da ke zuwa mata daga kasashen yammacin Turai ta ce dakarunta na ci gaba da kasancewa cikin karsashi a birnin Mariupol da Rasha ta daidaita.

Rasha ta yi ikirarin kwace birnin Mariupol, wanda ke da mahimmanci ga dabarunta na yakin da ta fara kusan watanni 2 da suka gabata, bayan da shugaba Vladimir Putin ya yi umurnin mamayar Ukraine da ke neman kulla dangantaka da Turai.

Wani babban hafsan sojin Rasha, Manjo Janar Rustam Minnekaev ya ce tun da Rasha ta shiga kashi na 2 na mamayar Ukraine, daya daga cikin manya burukan da ta sanya a gaba shine tabbatar da cikakkaken iko da garin Donbas da kuma kudancin Ukraine, abin da ke nuni da cewa har yanzu da sauran rina a kaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.