An tara wa Ukraine kudin ci gaba da fada da Rasha
An tara sama da Euro biliyan 6 a wani taro da aka gudanar a birnin Warsaw da zummar tallafa wa kasar Ukraine don ci gaba da yaki da Rasha.
Wallafawa ranar:
Firaministan Poland Mateusz Morawiecki ya sanar da tallafin, yana mai cewa, za a yi amfani da kudin wajen agaza wa Ukraine da kuma sauran masu mara wa kasar baya a daidai lokacin da take yaki da Rasha.
Firaministan ya ce, wannan taron tallafin ya nuna wani gagarumin hadin-kai a tsakanin kasashen Turai da suka kawo gudun-mawar a daidai lokacin da Rasha ta kai mutuwa a can Ukraine a cewarsa.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi jawabi ta kafar bidiyo a taron wanda kasashen Poland da Sweden da kungiyar Tarayyar Turai suka shirya.
Firaministan na Poland ya kuma bukaci kungiyar Tarayyar Turai da ta bai wa Ukraine matsayi na mamba a cikin kungiyar ta EU kamar dai yadda aka yi kasar alkawari.
A yayin gudanar da wannan taro, Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta sanar da bada tallafin Euro miliyan 200 a matsayin wani sabon tallafi ga mutanen Ukraine da suka rasa muhallansu sakamakon farmakin Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu