Isa ga babban shafi
Faransa-Macron

An rantsar da Macron don yin wa’adi na 2 a matsayin shugaban Faransa

An rantsa da shugaban Faransa  Emmanuel Macron a yau Asabar don yin wa’adi na 2 a matsayin shugaban Faransa bayan da ya kada jam’iyyar masu tsatsauran ra’ayi a zaben da aka yi a watan Afrilu.

Sugaban Faransa Emmanuel Macron yayin da yake sanya hannu a kundi bayan rantsar da shi don yin wa'adi na 2 a Asabar.
Sugaban Faransa Emmanuel Macron yayin da yake sanya hannu a kundi bayan rantsar da shi don yin wa'adi na 2 a Asabar. REUTERS - GONZALO FUENTES
Talla

A wani biki  da aka yi a fadar gwamnatin kasar, Elysee, shugaban kwamitin tsarin mulkin kasar Laurent Fabius ya tabbatar da macron a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasa na watan Afrilu, daga nan shugaban ya sanya hannu a takardar ranstarwa.

Bikin da ya samu halartar ‘yan daruruwan mutane ciki har da mai dakinsa Brigitte da kuma tsaffin shugabannin Faransa da ke raye, Francois Hollande da Nicolas Sarkozy,ya kasance karon farko da waw ani shugaban kasar ya lashe zaben don yin wa’adi na 2 a cikin shekaru 20.

Shugaban na fuskantar kalubale iri iri a cikin da wajen kasar, biyo bayan wa’adi na farko da ya yi, wanda ya kawo rarrabuwar kawuna a kasar.

Macron na fuskantar jan aiki na aiwatar da sauye sauye da ya  alkawarta a lokacin da ya hau karagar mulki a matsayin shugaban kasar Faransa ma fi karancin shekaru a shekarar 2017, ciki har da kalubalen mamayar da Rasha ke yi a Ukraine.

A jawabin da ya gabatar, bayan rantsar da shi, Macron ya sha alwashin gudanar d mulkin da zai ja kowa a jiki, bayan da masu wasu suka yi korafin cewa salon mulkinsa a  matsayin  mai tsauri, kuma irin na masu jijji da kai.

Bikin rantsar da shugaban na Faransa ya yi kamanceceniya da na shugaba Francois Mitterrand a shekarar1988 da  Jacques Chirac a shekarar 2002, shugabannin kasar na karshe da suka samu nasarar yin wa’adi na 2 kafin Macron, ganin cewa babu shawagin motoci da shimfida da sauran abubuwan kasaita.

Macron zai fara wa’adi na biyu ne a ranar 13 ga watan Mayu, lokacin da na farkon zai kare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.