Man City ta kama hanyar lashe gasar Firimiya a Ingila
Kungiyar Manchester City ta lallasa Newcastle United a gasar Firimiya ta Ingila da ci 5-0 abinda ya dada bata damar matsawa kusa da kofin gasar, yayin da Liverpool ta barar da damar ta jiya a karawar da suka yi da Tottenham wanda ya tashi 1-1.
Wallafawa ranar:
City ta zazzagawa Leeds kwallaye 5 ta hannun Raheem Sterling da Aymeric Laporte da Rodri da kuma Phil Foden nasarar da ta bata damar baiwa Liverpool rata da maki 3 a teburin Firimiya.
Kungiyar Chelsea na ci gaba da zama a matsayi na 3 da maki 67, yayin da Arsenal ke matsayi na 4 da maki 66, sai kuma Tottenham da maki 62 a matsayi na 5, Manchester United na matsayi na 6 da maki 58.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu