Isa ga babban shafi
Faransa-Fillon

Kotun daukaka kara a Faransa ta tabbatar da hukuncin dauri kan Francois Fillon

Kotun daukaka kara a Faransa ta tabbatar da hukuncin farko da kotun Paris ta zartas kan tsohon Firaministan kasar Francois Fillon game da badakalar aikin mai dakinsa da ya kai ga biyanta miliyoyin yuri daga baitilmalin kasar.

Tsohon Firaministan Faransa François Fillon.
Tsohon Firaministan Faransa François Fillon. © Charles Platiau, Reuters
Talla

A zaman sauraran daukaka karar na jiya litinin kotun ta sassautawa Francoise Fillon hukuncin zuwa shekaru 4 daya kunshi 3 a gida, daga hukuncin farko na shekaru 5 dake kunshe da 3 a waje.

A shekarar 2017 ne wannan badakala ta bayyana lokacin da Fillon ke sahun gaba a jerin ‘yan takarar neman kujerar shugabancin Faransa, batun da ya fusata al’ummar kasar yayinda aka fara yi masa shari’a tare da zatas masa da hukunci a shekarar 2020.

Hukuncin kotun ya kuma bukaci Fillon da mai dakinsa su biya tarar yuro dubu dari 8 ga majalisar kasar yayinda ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 3 da tun farko kotu ta zartaswa Marc Joulaud mutumin da aka samu da laifin bayar da aikin ga Penelope Fillon mai dakin tsohon shugaban tsakanin shekarun 1998 zuwa 2013 matsayin mataimakiyar majalisa.

Kotun daukaka karar ta zartas da wannan hukunci ba tare da halartar ilahirin mutanen da ake zargi ba, ko da yak e lauyoyinsu sun sha alwashin daukaka kara a kotun koli don kalubalantar hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.