Manchester United zata raba gari da Juan Mata a cikin wannan wata
A karshen wannan wata ne dan wasan kasar Spain Juan Mata zai kawo karshen kwantargin sa da kungiyar Manchester United a karshen wannan watan da muke cikin sa.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta Manchester United ce ta fitar da wannan labari, kungiyar ta kuma sanar da ficewar wasu daga cikin yan wasan ta da suka hada Paul Pogba da Jesse Lingard, yayinda wasu daga cikin yan wasan kungiyar da suka hada Nemanja Matic da Edinson Cavani zasi fice a tsakiyar kaka.
Juan Mata ya bayyana sanye da rigar kungiyar ta Manchester United sau 285 tareda lashe kofuna sau uku tun bayan zuwan sa wannan kungiya ta Manchester United daga kungiyar Chelsea a kan kudi milyan 43 na kudin Euros.
A karshe kungiyar ta Manchester United ta wallafa a shafinta cewa muna godiya bayan share shekaru 8 da United Juan, da sunan kungiyar muna maka fata na gari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu