Isa ga babban shafi

Turai ta hana sayen danyen man Rasha, da sanya wa budurwar Putin takunkumi

Kungiyar tarayyar Turai ta hana shigar da danyen mai daga Russia zuwa yankin a hukumance, abin da ke zama takunkumi mafi muni da aka sanyawa Russia, tun bayan da ta fara kutsen ta a Ukraine.

Turai ta haramta sayen danyen man Rasha a hukumance.
Turai ta haramta sayen danyen man Rasha a hukumance. © REUTERS/Richard Carson/File Photo
Talla

Baya ga wannan takunkumin, kungiyar tarayyar Turan ta kuma kakaba wa wata mata, wadda aka ce budurwa Vladmir Putin ce, mai suna Alina Kabaeva takunkumi, tare da hana ta amfani da duk wata kadara tata dake kasashen waje, da dakatar da takardar shige da ficenta na biza, sannan kuma aka sanya ta a jerin mutane masu hadari a duniya.

Tarayyar Turan ta kuma kakaba wa wasu manyan dakarun sojin Russia makamancin takunkumin, sakamakon zargin su da hannu a kisan kare dangin da aka yi wa jama’ar Bucha.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kasar Hungary ta amince da bukatar tarayyar Turan na kakaba wa Russia takunkumin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.