Isa ga babban shafi

Rasha ta ci ribar kusan yuro biliyan ɗari a cinikin mai a kwanaki 100

Wani bincike ya bayyana cewar Rasha ta ci ribar Yuro biliyan 98 daga man da take sayarwa a kasashen duniya a cikin kwanaki 100 da aka kwashe ana yakin Ukraine, kuma akasarin man an kai shi kasashen Turai ne.

Bututun mai dake tsakanin Rasha da kasar Hungary.
Bututun mai dake tsakanin Rasha da kasar Hungary. REUTERS - BERNADETT SZABO
Talla

Rahotan binciken da Cibiyar Binciken makamashi ta CREA dake Finland ta gudanar na zuwa ne a daidai lokacin da Ukraine ke kara kira ga kasashen Yammacin duniya da su kawo karshen duk wani cinakayyar dake tsakanin su da Rasha domin hana ta samun kudade.

Katse tsayen mai

A farkon wannan watan, kungiyar kasashen Turai ta amince da shirin katse sayen mai daga Rasha wanda nahiyar ta dogara akai, duk da yake kungiyar na shirin rage cinikin iskar gas na kashi biyu bisa uku akan yadda ta saba saye.

Rahotan binciken yace kasashen Turai sun sayi kashi 61 na man da Rasha ke fitarwa a cikin kwanaki 100 da aka kwashe ana yakin Ukraine wanda kudin sa ya kai yuro biliyan 57.

Kasar China

Kasar China ita tafi sayen mai a Rasha da kudin sa yakai yuro biliyan 12.6 sai kasar Jamus mai euro biliyan 12.1 sannan Italia mai euro biliyan 7.8.

Rahotan binciken yace Rasha tafi samun kudin shigar ta daga bangaren man fetur da kudin sa ya kai euro biliyan 46, sai iskar gas da kayayyakin da ake fitarwa daga albarkatun mai sannan gawayi.

Raguwar kasuwanci

Binciken yace kayayyakin da Rasha take fitarwa zuwa kasuwannin duniya sun ragu, sakamakon yadda kasashen duniya suka juya mata baya saboda mamayar Ukraine, amma hakan bai hana ta samun kudade ba saboda yadda farashin makamashin ya tashi a kasuwannin duniya.

Daga cikin kasashen da suka kara yawan makamashin da suke saya daga Rasha akwai China da India da Daular Larabawa da kuma Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.