Isa ga babban shafi

Amurka za ta mikawa Ukraine karin tallafin makamai na dala biliyan 1

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da sabon shirin gwamnatinsa na mikawa kasar Ukraine tallafin karin makaman da darajarsu ta kai dala biliyan daya.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. REUTERS - JOSHUA ROBERTS
Talla

Matakin na Amurka ya biyo bayan rokon karin tallafin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy yayi a baya bayan nan domin karfafawa dakarunsa gwiwa dake fafatawa da na Rasha.

Sai dai wasu daga cikin masu sharhi kan lamurran dake wakana, sun yi gargadin cewa tarin makaman da Amurka da sauran kasashen Turai ke baiwa Ukraine a matsayin tallafin yakar Rasha, ka iya zama kalubale babba ga tsaro a sassan Turai nan gaba, la’akari da rahotannin yiwuwar fantsamar da makaman ke yi zuwa wuraren da ba a yi nufin su kai ba.

Cikin makwannin baya bayan nan dakarun Rasha suka bayyana cewa suna dab da kammala kwace iko da Severodonetsk, wani muhimmin birni mai arzikin masana'antu a yankin Lugansk da sojojin Ukraine suke ta kokarin karewa.

Samun nasarar kame birnin Severodonetsk ya zama babban burin Rasha, la’akari da cewar shi ne zai zama  hanyar zuwa wani babban birnin mai suna Sloviansk dake yankin Kramatorsk.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.