Isa ga babban shafi

EU ta amince da baiwa Ukraine damar fara takarar shiga cikinta

Hukumar gudanarwar Tarayyar Turai ta amince da baiwa kasar Ukraine da yaki ya daidaita damar zama ‘yar takarar neman shiga kungiyar EU, matakin da ka iya budewa kasar cimma burin zaman mamba a kungiyar ta kasashen Turai, kodayake za a iya shafe tsawon shekaru kafin hakan ya tabbata.

Tutociin kungiyar kasashen Turai EU a birnin Brussels.
Tutociin kungiyar kasashen Turai EU a birnin Brussels. REUTERS - Francois Lenoir
Talla

Shugabar kungiyar ta EU Ursula von der Leyen ce ta bayyana matsayar da aka cimma a karshen makon nan.

A mako mai zuwa shugabannin kasashe 27 dake karkashin EU za su tattauna kan damar da aka baiwa Ukraine, yayin taron da za su yi a birnin Brussels.

Sai dai wasu kasashen Tarayyar Turai irinsu Netherlands na ci gaba da nuna shakku kan tursasa karbar Ukraine cikin gaggawa, yayin da jami'an diflomasiyya suka ce suna sa ran shugabannin za su rattaba hannu kan amincewa da matakin na farko, dangane da bata damar takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.