Isa ga babban shafi

EU ta amince bai wa Ukraine da Moldova damar zama mambobinta

Shugabannin Tarayyar Turai sun amince da bai wa Ukraine da Moldova da ke fama da yaki, takarar shiga Kungiyar EU a wani mataki na nuna goyon bayansu kan mamayar da Rasha ta yiwa kasar.

Wasu daga cikin magoya bayan shiga kasar Uktraine tarrayar Turai
Wasu daga cikin magoya bayan shiga kasar Uktraine tarrayar Turai AFP - KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Shugaban EU Charles Michel yayin wani taron koli a Brussels, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa wani muhimmin mataki ne da aka baiwa kasashen na shiga Kungiyar.

Tuni shugaban Ukraine din Volodymyr Zelensky ya jinjinawa shugabannin turai bisa wannan dama.

Tabbatar da matsayin shiga takara shine matakin farko na shiga EU, tsarin da ke daukar shekaru kafin kasa ta zama mamba.

Rasha dai na gab da kwace manyan biranen Severodonetsk da Lysychansk da ke yankin gabashin Donbas na Ukraine, kuma karbar biranen biyu zai baiwa kasar ikon daukacin Lugansk, daya daga cikin yankuna biyu masu makwabtaka da Donetsk wanda ke da cibiyar masana'antar Ukraine ta Donbas.

Yanzu haka dai Jamus na neman mafita game da batun iskar gas, bayan ta samu katsewar  sa daga rashan, bayan da wasu kasashen Turai suka yanke alakar kasuwancin gas din da Rasha saboda kin biyan ta da kudin ruble.

Yayin da shugaban Amurka Joe Biden zai gana da shugabannin Birtaniya, Canada, Faransa, Jamus, Italiya, da Japan a taron da za a yi a Bavaria kafin ya tafi Madrid don halartar taron NATO,

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kira ga shugabannin kasashen Brazil, Indiya, China da Afirka ta Kudu da suka kasance abokan kawancen Rasha a kungiyar da ake kira BRICS da su ba ta hadin kai domin tunkarar takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.