Isa ga babban shafi

Dakile 'yancin zubar da ciki a Amurka koma baya ne ga 'yancin dan adam - MDD

Shugabar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet, ta ce matakin kotun kolin Amurka na yanke hukuncin kawo karshen 'yancin zubar da ciki "babban koma baya ne ga 'yancin dan adam da daidaiton jinsi.

Shugabar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet.
Shugabar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet. AP - Martial Trezzini
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar tsohuwar shugabar ta kasar Chile, ta ce fiye da kasashe 50 masu tsauraran dokoki ne suka sassauta dokar zubar da ciki a cikin shekaru 25 da suka gabata, to amma hukuncin ranar Juma’a, ya sanya Amurka juya baya ga cigaba da aka samu.

Hukuncin kotun kolin Amurkan dai bai tsaye bai haramta zubar da ciki ba, sai dai ya mayar da Amurka kan matakin da take kafin babban hukunci Roe v. Wade a shekarar 1973, lokacin da kowace jiha ke da 'yancin ba da damar zubar da ciki ko kuma haramtawa.

A sakon da ya fitar a shafinsa na Twitter, tsohon shugaban Amurka Barrack Obama, ya bayyana hukuncin tamkar kai hari ne kan muhimman ginshikai na ‘yancin dan adam a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.