Isa ga babban shafi

Ukraine ta kashe fursunonin yaki da dama a harin da ta kai Donetsk - Rasha

Rundunar sojin Rasha tare da ‘yan awaren da ke samun goyon bayan kasar sun zargi dakarun  Ukraine da kai kari kan wani gidan yarin da ta garkame fursunonin yaki da take tsare da su a  gabashin kasar, tana mai cewa gwammai sun mutu, da dama kuma sun samu raunuka.

Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Shugaban Rasha Vladimir Putin. via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce an kai har ikan gidan yarin da ake tsare da fursunonin yaki a yankin Donetsk  da ke hannun ‘yan aware a gabashin Ukraine da rokoki samfurin HIMARS da aka kera a Amurka.

Sanarwar ta ce fursunonin yaki 40 ne suka mutu, a yayin da 75 suka jikkata, ta kuma kara da cewa ma’aikatan gidan yarin 8 sun samu raunuka.

An samu alkalumma masu cin karo da juna a game da wadanda suka mutu, inda a yayin da jagoran ‘yan awaren Donetsk,  Denis Pushilin, ya ce mutane 47 ne suka mutu,  rundunar mayakan ‘yan awaren ta Territorial defence forces  ta ce 53 suka mutu.

Jimillar fursunonin yaki 193 ne ke tsare a wannan  gidan yarin a lokacin da aka kai harin a cewar    Pushilin a yayin wani jawabi da aka wats a tashar talabijin Rasha.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce fursunonin yakin yakin, wadanda ‘yan kasar Ukraine ne sun hada da dakarun bataliyar Azov wadanda suka kare wani yanki na na birnin Mariupol mai tashar jirgin ruwan.

A watan Mayu ne aka yi mayakan Ukraine 2500 kawanya bayan shafe makonni ana bata kashi birnin Mariupol.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.