Isa ga babban shafi

IAEA ta bukaci wanzuwar jami'anta a tashar nukiliyar Ukraine ta Zaporizhzhia

Hukumar kula da Makamashin nukiliya ta duniya na bukatar zaman din-din-din a babbatar tashar Nukiliyar Turai ta Zapharosia dake Ukraine, sakamakon barzanar kasancewar Dakarun Russia kadai a gurin bayan da suka kwace iko da ita, wattanin da suka gabata.

Babbar tashar nukiliyar Ukraine.
Babbar tashar nukiliyar Ukraine. REUTERS - ALEXANDER ERMOCHENKO
Talla

Bukatar hakan ta zo ne bayan da wakilai da masu sanya idanu daga majalisar dinkin duniya ke shirin kai ziyara tashar nukiliyar Zapharosia din, yayin da suka ce zaman su a gurin zai rage hadarin da kasancewar dakarun Russia kadai ka iya haddasawa.

A cewar hukumar ta IAEA bukatar ta kawai shine ceto duniya daga Fushin Russia, wadda take-taken ta ke nuna cewa kowanne lokaci zata iya harar tashar Nukiliyar wanda kuma hakan zai zama babban bala’i ga duniya.

Har ya zuwa yanzu dai ana zarigin Russia da ci gaba da kai hare-haren makamai masu linzami a yankunan da ke gab da babbar tashar Nukiliyar, yayin da IAEA ke nuna fargabar subucewar makami ya fada tashar.

Duk da dai wannan zargi ne da Russia ta sha musantawa, yayin da ta ke jefa shi Dakarun kan Ukraine, amma dai batun na kara jan hankalin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.