Isa ga babban shafi

'Yan ci-rani sun mamaye wani katafaren gini a Paris

Duruwan bakin haure marasa matsuguni a Faransa masamman ‘yan asalin Afirka da Afghanistan, sun yi  mamaye wani gini da babu kowa a kudancin birnin Paris a wannan Lahadi, kafin ‘yan sanda su afka musu

Jami'an 'yan sanda sun fatattaki 'yan ci-ranin daga bisani
Jami'an 'yan sanda sun fatattaki 'yan ci-ranin daga bisani AP - Edgar H. Clemente
Talla

Wata kungiya da ke taimaka wa baki ta United Migrants ta ce, wadannan ‘yan ci-ranin kimamin 300 zuwa 400 da suka hada da 'yan kasar Ivory Coast da Chadi da kuma Sudan, sun shiga cikin katafaren ginin ne mai girman murabba'in mita dubu 8 a Gentilly tun cikin daren Asabar, inda suka sadaukar da kansu ga halaka don nuna adawa da matakin korar su daga kasar.

'Yan sandan sun yi kokarin kwashe da dama daga cikinsu, amma har ya zuwa maraicin ranar Lahadi akwai wasu da suka nuna tirjiya inda suka yi kememe ba za su fice ba, yayin da wasu ma suka haura kololuwar ginin inda suke barazanar za su hallaka kansu muddun aka ci gaba da matsa musu lamba.

United Migrant ta ce, bakin-hauren da suka hada da mata da kananan yara, na zanga-zangar adawa ne da matakin gwamnatin na shirin korar su bayan da suka zarce wa’adin zama ba tare da matsuguni ba da aka tsawaita musu lokacin a baya.

Ma’aikatar Karamar Hukumar ta ce, ba za a amince su yada zango a ginin ba, saboda hadarin da ke tattare da zama a wajen da ko wutar lantarki babu ballantana ruwan sha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.