Isa ga babban shafi

Dabara ta rage ga mai shiga rijiya kan yarjejeniyar nukiliyar Iran - Faransa

Ministar harkokin wajen Faransa ta yi kira ga Iran da ta karbi tayin da aka gabatar mata a game da batun farfado da yarjejeniyar nukiliya, tana mai gargadin cewa ba za ta samu abin da ya zarce wanda aka mika mata ba.

Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna.
Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna. © AFP / BENOIT TESSIER
Talla

A daidai lokacin da ake bude babban  taron majalisar dinkin, duniya na shekara shekara, ministar harkokin wajen ta Faransa, Catherine Colonna ba ta yanke kaunar cewa shugaba Emmanuel Macron zai gana da takwaransa, Ebrahim Raisi ba, tana mai cewa za su zura ido su ga abin da zai kasance a wannan mako.

Sai dai ministar, wadda ta yi nuni da cewa babu wani tayi da ya kai wannan armashi a yanzu,   ta ce damar na daf da gushewa, inda ta ce shawara ta rage ga Iran.

A ganawar da ya yi da wata kafar talabijin ta Amurka, shugaban Iran, Ebrahim Raisi, ya ce kasarsa a shirye take ta amshi tayi mai armashi, amma kuma dole shugaba Joe Biden ya ba shi tabbacin cewa Amurka ba za ta yi watsi da yarjejeniyar a karkashin sabon shugaba a nan gaba, ba, abin da Amurkar take ganin ba zai yiwu ba.

Tsohon shugaba Donald Trump ne ya janye Amurka daga yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran ta shekarar 2015, wadda a karkashinta Iran din ta rage aikin tace makamashin nukiliyarta bisa alkawarin sassauta mata jerin takunkuman da aka lafta mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.