Isa ga babban shafi

Rasha ta yi wa Faransa kashedi kan taimakawa Ukraine da makamai

Rasha ta gargadi Faransa a game da gudunmawar makamai da take bai wa Ukraine a yakin suke gwabzawa, abin da ta ce bai dace ba.

Shugaban Rasha Vladimir Poutine.
Shugaban Rasha Vladimir Poutine. AP - Sergei Bobylev
Talla

Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar ta ce ganawa tsakanin mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Alexander Grushko da jakadan Faransa a Moscow Pierre Levy, ta mayar da hankali ne a kan rashin dacewar tallafa wa Ukraine da makamai.

Sun kuma tattauna yadda ake aiwatar da yarjejeniyar fitar da hatsi da kuma matsalolin da ake cin karo da su wajen tabbatar da wadatuwar abinci a duniya.

A makwannin baya bayan nan shugaban Rasha Vladimir Putin ya zargi kasashen Turai da yaudara dangane aiwatar da yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine zuwa sassan duniya.

Putin ya ce akasarin kayayyakin abincin da aka fitar daga Ukraine na tafiya ne ga kasashen Turai, a maimakon kasashe matalauta a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.