Isa ga babban shafi

Dakarun Rasha da na Ukraine za su sake gwabza fada gaba da gaba a yankin Kherson

Fadar shugaban kasar Ukraine ta ce dakarun Rasha sun kame muhimman sassan yankin Kherson da ke kudancin kasar dai dai lokacin da dakarun Ukraine ke gab da isa yankin a wani yanayi da za a iya sake fuskantar mummunar gwabzawa tsakanin bangarorin biyu.

Wasu dakarun Rasha da ke yaki a Ukraine.
Wasu dakarun Rasha da ke yaki a Ukraine. REUTERS - Alexander Ermochenko
Talla

A wani jawabinsa ta faifan bidiyo mashawarcin fadar shugaban kasar ta Ukraine Oleksiy Arestovich ya ce Rasha ta tattara karfin dakarunta a yankin na Kherson lamarin da ka iya zama gwabzawa ta gaba da gaba mafi muni da bangarorin biyu za su yi a baya-bayan nan.

Duk da cewa Arestovich bai fayyace hakikanin lokacin da ake shirin gwabza sabon yakin ba amma ya bada tabbacin cewa dakarun sun tukari inda Sojin Rasha suka yi sansani kuma babu shirin juya baya.

Kalaman na Arestovich na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaba Joe Biden na Amurka ke gargadin shugaba Vladimir Putin game da shirin kai harin nukiliya a sassan Ukraine, inda ya bayyana cewa duk wani yunkurin kai farmakin Nukiliya zai zama mafi munin kuskure da Rasha ba ta taba yi ba a tarihi.

A cewar Biden akwai munanan shirye-shirye da Rasha ke shirin aiwatarwa ciki har da amfani da bama-baman nukiliya a cikin Ukraine wanda kuma ba zai haifar da da mai ido ba.

Alkaluman da Amurka ta fitar sun nuna cewa zuwa yanzu Rasha ta yi asarar sojojin da yawan kai dubu 60 zuwa dubu 80 a Ukraine lamarin da ya fusata ta har take yunkurin kai harin na Nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.