Isa ga babban shafi

Amurka: Rinjayen jam'iyyar Democrats a majaliar dokoki na fuskantar barazana

Amurkawa sun kada kuri’a a zaben tsakiyar wa’adi da aka yi a Talata, zaben da ke barazana ga kwarya-kwaryar rinjayen da jam’iyyar Democrats mai mulkin kasar ke da shi a majalisun dattawa da na wakilai, bayan da aka rufe rumfunan zabe cikin tsakiyar dare a kasar.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Zaben na Talata ne dai zai tantance yadda makomar jam’iyyar Democrats za ta kasance a majalisun dokokin kasar, inda a halin yanzu take kokarin jaddada kwaryar-kawaryar rinjayen da take da shi a majalisar dattawa.

Hasashen kafafen yada labarai dai na nuni da cewa jam’iyyar adawa ta Republican za ta iya samun rinjaye a majalisar wakilai, amma a majlisar dattawa tana kasa tana dabo, duba da cewa akwai wasu mahimman kujeru masu mahimmanci da ba a iya tantance wadanda suka lashe su.

Yanzu dai hankalin jam’iyyar Democrats mai mulki ya tashi, biyo bayan rahotannin da ke cewa J.D Vince, mawallafin littafin nan da ya yi fice, wato "Hillbilly Elegy" mai samun goyon bayan tsohon shugaba Donald Trump, ya lashe zaben majalisar dattawa a Ohio, lamarin da ya tada hankalin jam’iyyar Democrats ta Joe Biden.

Sai dai wannan nasara ba ta nufin karin gurbi ga Republican, saboda dan Republican, Rob Portman ne ya yi murabus daga kujerar.

A yayin da aka rufe rumfunan zabe, ana ci gaba da dakon sakamako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.