Isa ga babban shafi

Wata kotun Amurka ta kori karar Yeriman Saudiyya kan zargin kisan dan jarida Khashoggi

Wani alkali a Kotun Amurka ya yi watsi da karar da aka shigar kan yarima mai jiran gado na sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman kan wadda ake zarginsa da hannu a kisan dan jarida, Jamal Khashoggi a shekarar 2018.

Yeriman Saudiya mai jiran gado, Mohamed Ben Salman.
Yeriman Saudiya mai jiran gado, Mohamed Ben Salman. AFP - HO
Talla

Alkalin kotun tarayya a birnin Washington, John Bates, ya yanke hukuncin ne la’akari da matsayar gwamnatin Amurka na cewa Yarima Mohammed, wanda aka nada firaministan Saudiyya a watan Satumba, na da kariya a kotunan Amurka a matsayinsa na shugaban wata kasar waje.

Bates ya ce a karar da uwargidar Khashoggi,Hatice Cengiz da kungiyarsa ta fafutuka DAWN suka shigar, sun kawo shaidu masu karfi da ke nuni da cewa yerima Mohammed bi Salman yana da hannu a kisan dan jaridar.

Amma sai ya e bas hi da ikon yin watsi da matsayar gwamnatin Amurka ta ranar 17 ga watan Nuwamba, inda ta ce Yerim bin Salman yana da kariya a matsayinsa na shugaban wata kasar waje.

Yerima Mohammed bin Salman ya kasance mai jiran gado na tsawon lokaci a karkashin mahaifinsa, Sarki Salman.

Daya daga cikin wadanda suka fi caccakar yeriman shine, dan jarida, Jamal Khashoggi, mazaunin Amurka, wanda aka kashe a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santambul na Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.