Isa ga babban shafi

Faransawa sun matsa wa gwamnati kan dokar fansho

Gwamnatin Faransa ta ce, akwai yiwuwar ta yi sassauci kan shirinta na kara shekarun ritaya zuwa 65, a daidai lokacin da ‘yan kasar ke adawa da shirin sauya dokokin fansho da shugaba Emmanuel Macron ya bijiro da shi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP - Christophe Simon
Talla

Firaministar Faransa Elisabeth Borne da ke magana gabanin gagarumar tattaunawa da kungiyoyin kwadagon kasar ta shaida wa gidan Radio na FranceInfo cewa, ba wai sun buga hatimi ba ne kan dole a tsayar da shekaru 65 a matsayin shekarun ritaya a kasar.

Uwargida Borne ta kara da cewa,  akwai sauran hanyoyin lalubo bakin zaren da za su iya taimaka wa gwamnati cimma muradinta na daidaita tsarin fansho nan da shekara ta 2030.

A ranar 23 ga wannan wata na Janairu ne za a gabatar da tsarin na fansho ga majalisar ministocin kasar kafin daga bisani a tafka muhawa a kai a zauren majalisar dokoki a farkon watan Fabairu kamar yadda Borne ta yi karin haske.

Su dai kungiyoyin kwadago sun fito karara sun nuna adawarsu ta kara yawan shekarun ritaya daga shekara 62 zuwa 65, amma gwamnatin Macron ta nuna kafiya saboda dalilai na magance matsalar gibi a kasafin kudin kasar a cewarta.

Kashi 54 na al’ummar Faransa sun ce, sam ba su yi na’am da sabon tsarin na fansho ba kamar yadda kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a ta nuna a Litinin din nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.