Isa ga babban shafi

Dan bindiga ya sake kashe mutane a California

‘Yan sanda a Amurka sun cafke wani ma'aikacin gona dan asalin yankin Asiya, bayan da ya kashe abokan aikinsa bakwai a gaban yara a wasu wurare biyu da ke arewacin jihar California.

Dan bindigar da ake zargi da akshe mutane 7 a arewacin jihar California, da ke Amurka.
Dan bindigar da ake zargi da akshe mutane 7 a arewacin jihar California, da ke Amurka. via REUTERS - ABC AFFILIATE KGO
Talla

Sabon tashin hankalin ya zo ne ‘yan kwanaki, bayan da wani dan bindiga ya kashe mutane 11 a wani bikin sabuwar shekara a kusa da birnin Los Angeles a dai Californian.

Asarar rayukan da Amurkawa 'yan asalin nahiyar Asiya suka sake fuskanta jihar ta California sun faru ne a wasu gonaki biyu da ke kusa da Half Moon Bay, wani yanki na gabar teku kusa da birnin San Francisco.

Shugaban ‘yan sandan gundumar San Mateo Christina Corpus ya ce mutane bakwai suka mutu, yayin da mutum daya ya jikkata sakamakon tagwayen harbe-harben na ranar Litinin, tuni  kuma  suka kama wani wani mutum mai suna Chunli Zhao mai shekaru 67 mazaunin yankin Half Moon Bay.

Wannan tashin hankali ya zo ne a dai dai lokacin da, jami’an tsaro a kudancin jihar California suke bincike kan abin da ya sanya wani tsoho dan gudun hijira shi ma dan asalin nahiyar Asiy, harbe mutane 11 har lahira, a yayin da ake taro a wani dakin raye-raye na bayan gari, kafin daga bisani shi ma ya kashe kansa yayin da ‘yan sanda suka rufar masa.

Binciken jami’an tsaro dai ya gano cewar, dukkanin wadanda ‘yan bindigar da suka yi aika-aikar sun yi amfani da bindigogi ne masu sarrafa kansu yayin hare-haren da suka kai, kuma dukkansu akwai hujjoji da ke nuna cewar suna da alaka da a kalla wasu daga cikin wadanda suka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.