Isa ga babban shafi

Turkiyya ta kawo karshen aikin ceton mutanen da girgizar kasa ta rutsa da su

Hukumar bada agajin gaggawa ta Turkiyya ta sanar da kawo karshen ayyukan taimako da laluben wadanda baraguzan gine-gine suka danne a sanadin girgizar kasar da ta afkawa kasar.

Yadda aikin ceto ya kasance a Turkiyya
Yadda aikin ceto ya kasance a Turkiyya AP - Khalil Hamra
Talla

Makkonni biyu da suka gabata, kawo yanzu an gano gawarwaki dubu 40,642 a aikin ceto da aka rika yi domin lalubo masu rai da kuma gawawakin da gine-gine suka danne.

Gwamnatin kasar ta ce kawo yanzu an kammala aiki da kusan kaso 90 cikin dari, wanda ya fadawa arewacin kasar da ke iyaka da Syria, da ya kashe mutane sama da dubu 45 a kasashen biyu.

Bayanai sun ce kawo yanzu girgizar kasar ta raba miliyoyin mutane da muhallan su, dai-dai lokacin da ake fama da tsananin sanyi a kasar, baya ga tashin farashin kayayyaki da rashin kudade a hannun jama’a sanadin girgizar kasar.

Alkalma sun nuna a Syria yanzu an samo gawarkin mutane dubu 5,800, a aikin ceto dake tafiyar wahainiya a kasar saboda batutuwan da suka shafi siyasa da sauran matsaloli.

A yanzu dai hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya ta ce akalla mutane miliyan 26 a kasashen biyu na bukatar agajin gaggawa na guraren kwana, kayan dumama jiki, abinci da kuma magunguna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.